RAHMA'S POV
Tunda muka fita na kasa sakewa. Mus'ab sai magana yakemin ƙasa ƙasa nikuma naƙi kulashi.
Inajin mamanshi da Abdallah sai hira sukeyi suna dariya. Dama Abdallah ba baya ba wajen surutu. Dana lura hankalinta baya kanmu cikin magana mai kaman raɗa na fara wa Mus'ab magana.
"Are you insane? Meyasa zaka shirya wannan abun baka faɗa min ba? What will umma asiya think of me now?"
Wani mugun murmushi yake yi kuma yaƙi amsa tambayoyi na. Leƙa mirror gabanshi yayi yana kallon Abdallah da mamanshi.
"Mom a ina zamu fara tsayawa?"
Tambayan na tayi ina nakeson a fara tsayawa.
Wallahi na daɗe banji na rasa abinda zan faɗa ba kaman yau.
"Mom a ko ina ma."
"A'a, ai wannan fitan naki ne. Sai inda kikace a fara tsayawa to nan za'a fara."
Yan yatsuna nake murzawa ba tsayawa na rasa ma ina zance. Dayake ba sanin wajajen nayi ba.
"Mom to mu fara tsayawa a coldstone. Kunyan ki takeji bazata faɗa ba. Amma ni ta daɗe da faɗa min tana maitan son ice cream" ya faɗa yana kallo na harda kanne min ido ɗaya.
Bugawa zuciya na yakeyi ba tsayawa cike da mamakin Mus'ab. Yaushe muka taɓa wannan hiran dashi da zai faɗi hakan sai Allah.
Murya ciki ciki na amsa da mu fara da nan ɗin.
Ta gefen ido na nake kallonshi yana driving kaman wani ɗan shekara 30. A nutsuwa da bin ƙa'idojin hanya.
Muna shiga Coldstone ya nemi waje yayi parking motan. Kafin in buɗe nawa ƙofan sai yayi sauri ya kulle daga wajenshi.
Da sauri na juya ina kallon baya dan inga reaction ɗin mamanshi. Ita kam har tasa kai tayi gaba.
Da sauri na juyo da kallo na kanshi.
"You look..... I don't even know what to say. Beyond beautiful. The word beautiful is a cliche and is not enough to describe you."
Wannan shine karo na farko dana fara jin wani yanayi a jikina.
Ji nayi wasu ƙananun tsutsotsi suna yawo a cikina. Da sauri na juya ina ƙokarin buɗe ƙofar motan.
Ɗan dariya yayi ya buɗe nashi naga ya juyo wajen da nake ya buɗe nawa ƙofan. Fitowa nayi ina kallon cikin idonshi. Wani murmushi yayi wanda yake ƙara mishi kyau.
Alamu yamin da mu fara tafiya domin su Abdallah kam har sun shige cikin wajen.
Tafiya nakeyi inajin ƙafofi na suna ƙoƙarin harɗewa. Wannan shine karo na farko da zanyi irin wannan fita ba tare da umma asiya ba.
Wanda nake iya tunawa munyi da Daddy da umma na tun ina ƙarama akasarin abinda ya faru na mantasu.
Muna shiga wajen ya nema min wajen zama tare da jamin kujera alamun in zauna. A hankali na zauna ina kallon wajen. Ɗan ɗurƙusowa yayi yana kallo na tare da ajiyan zuciya.
"Me za'a karɓo miki?" Yana faɗa sai wani murmushi yakeyi. Ni abin ma ya fara bani haushi.
Kallo inda mamanshi take nayi sai naga tana kallon mu. Da sauri na amsa mishi.
"Anything you are taking."
Cikin nutsuwa ya tafi domin karɓo mana ice cream ɗin.
Abdallah ne yake ta tsalle a hannun Maman Mus'ab. Suna zuwa kusa dani naji jiki na ya fara kyarma.
Murmushi tamin suka tafi seat ɗin baya na suka zauna.
Time to time Mus'ab yakan juyo mu haɗa ido sai yayi murmushi.

YOU ARE READING
AMJAD
RomanceAMJAD-Aikin da aka aiko ni zan iya yinshi kuwa? Tuntu?en da nayi a hanya bazai kawo min matsala cikin aikina ba? Zan iya ceto rayuwan dubbanin mutane da aka aiko ni kuwa? Ku biyoni cikin littafina mai suna AMJAD. Yana tattare da soyayya, matsalolin...