_____TAGWAYE BY BASMA_BASHIRKofar d'akin Maisha yake bibbigewa yana ambaton sunanta ahankali. Kwance take kan gado tana kunbu'ra haushi da damuwa sunyi mata yawa, jujjuyi take tin dazun ko zata samo mafita Amma dabarunta duk sun 'kare "babu wata mafita face ta tseyar da gidanta, ta tse madeideicin gida sannan tayi anfani da sauran kud'aden.
Ma'isha kibud'e, kud'i nakawo miki naira Million Uku kamar yedda kike bu'kata". Muryar Kawu Saminu data riski kunnuwarta ne yamatukar tsoratata, inda nan ta 'ke tamike koro'koro ta zaro idanuwarta a tsorace tabud'e masa kofa "Hey me kake anan? Kuma Wasu kud'ad'e kake magana, Ta fad'a ahankali.
Jakar dake hannunsa yamiko mata yanacewa: na saurari duk maganganun dakukayi da Mahaifiyarki cewa kina bu'katar kud'i kuma baki samo kud'aden awajen saba shine naciro nawa kud'aden dana tara nakawo Miki domin kiyi anfani dasu.Magana take muryarta ciki ciki domin kada wani yaji tattaunawar dasuke "Ba'nida bu'katar kud'ad'enka sabida Kai ba kowa bane awajena kuma ni Maisha ba matsiyaciya bace irinka kawai katafi kabani wuri.
"Ma'isha inaga har yanzu baki fahimci Mahaifinki bane, Yai saurin katseta: kwata kwata yanzu Sambo baya yi dake , kin rigada kin watsa masa 'kasa a ido babu inda kud'ensa suke 'karewa se gun Y'ar lelensa Ma'inah kuma gashi yakaita chan gidan d'aula da arziki tana more rayuwarta keko kina shan Bakar azaba anan.Me kake nufi? Ma'isha ta tambayesa cikin rud'ani. Bazaki ta6a ga'ne abinda nake nufi ba har tse kin ansa wannan kud'aden danayi niyar baki. Yafad'a ayayinda yake Miko mata jakar 'Idan kin ansa wa'innan kud'aden toh ko zakiji komai gamida Ma'inah kuma zan tsanar dake inda take ayanzu.
Ta6e Baki Maisha tai cikin mamaki tace' Bazan kar6i ko sisi daga wajenkaba sabida Na'fi 'karfin kaimin kyauta koda naira biyar ce wallahi matsayinda bata kai hakaba tukunna, the only solution shine ka tsei gidana Million Goma babu kari ba ragi sannan ne zan anshi kud'ad'enka. Murmushi Saminu yai 'Babu komai na yarda zan tse gidanki amma abisa sharad'i guda ko kad'an kada kisake kifad'awa Mahaifiyarki ko Mahaifinki har tse kin mallakamin takardun gidan.
Jinjina Kai tai "Deal na amince Kuma nima inada tawa sharad'i 'kada ka sake ka tsanar da Daddy Shirin mu kuma Koda kanunamin gidan daya 6oye Ma'inah kada ka tsanardashi Until I destroy her life bit by bit.
"Zaid why did you stop the car? Ma'inah ta tambayesa cikin mamaki. Babu mutsu ya amsa 'I want to make a call.
Ganin bai ta6a bata ansa kai tseye hakaba se yau yasa tai farin ciki har cikin zuciyarta, tana murmushi yayinda tace 'babu komai just make it fast kada mu makara.Jinjina kai yai shima yana murmushi.
"Kodei budurwarsa yake 'kira? Ma'inah ta tambayi 'kanta ahankali tace' Anyway koma wacece batayi dachen mijiba his such an arrogant.
"Helo Asad I'm sorry na d'an makara amma ina hany'an zuwa, yanzu Zan 'karaso ka tabbata ka'tara late comers, musamman sabbin ma'aikatan nan wanda zasu fara aiki yau because today is there first day in office bai 'kamata suyi latti ba.Shiru yai nad'an wasu mintuna sannan yace Good sunyi kokari and who among them is absent? kace Ma'inah Sambo Maidugu?
What? Kallonsa Ma'inah tai cikin rud'ani "Come on Zaid ba office d'in muke zuwa yanzu ba? Kafad'a masa Mana Asad is a good man he will definitely understand.Manna mata hauka yai "Alright Asad idan tashigo kawai kasa aturomin ita sama. Da wannan ya katse wayar sannan yafara tuki. Shiru Ma'inah tai tana binsa da kallo tareda mamakin halinsa babu wanda ya'kara cewa komai har tseda suka 'karaso. Motar tana tseyawa bo'sawansa suka bud'e, inda suka rufe masa baya ana binsa tamkar ya'fi kowa masayi a duniya.
Fitowa tai ahankali take tafiya har tseda ta 'karaso ciki, seketeriya ce tai mata magana "Ma'inah Sambo Maidugu why are you late? 'Daga ido tai takalleta sannan ta tasau'kar ahankali 'Im Sorry maam ba'nida lafiya shiyasa Amma... Just shut up you are not responsible at all, kitanadi bayananki zata anfaneki idan CEO ya tambayeki dalilin dayasa kikayi latti amasayinki na Masinjarsa.
