抖阴社区

                                        

Mama tashiga nan nan  da diyarta kanneta zagaye daita kowannesu Na murna ganinta hatta aunty Salma tazo da murnata wace ummi ce tasanar mata da zuwan Nablah din . gabadayansu ,suka saka nablah a tsakiyar su .suna murna da jin dadi ganinta .
nuratu ta kalli nablah  da kyau .
Kai Alhamdulilllahi yau dai zamu huta da shan zagi gurin baba.
Na aunty  Salma ta   tsiyar masa da "ya" nablah tayi  murmushi wanda ke karawa fuskarta kyau da annuri  tare da cewa  banana kennan.
nayi kewarsa nima sosai  fiyye da tunaninku ..

uhm kalli  yadda kika dawo Nablah  kinyi kyau dake  kikayi fresh sosai gadabaya fatar jikinki ta sauya  wlh  gurin nan ya amsheki inji cewar nuratu  ..
Allah ko  nablah tace hk tana murmushi sannan tacigaba duk wannan kyawun  da fresh din danayi wlh nafi son gidanmu koda kuwa za'a kwana bamu ci  ba Amman dai  zan koma sbd wani dalili nawa .. aunty Salma tayi saurin cewa wlh bada hannuna ba 'cikin komawarki .
Ni dai tunda kin dawo Na auna arziki Na huta da fadan baba  wlh  har fargaba zuwa gidan nan nake .
Tun tafiyarki nake 'cikin tashin hankali boye miki kawai nakeyi sbd kwanciyar naki hankalin Amman mgnr gsky Na tsorata da al'amarin baba..  nan nuratu tashiga zaiyanewa  nablah labarin duk abinda ya faru da yadda aunty Salma ke shiri idan zatazo gida .
aiko gabadayansu suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya .

Maman da  tun sanda suka fara hirasu  da nuratu da Salma  ba tsoma musu baki  ba sai yanzu tace uhmmmm nablah bana jin babanki zai yarda ki sake barin gidan nan ballanantana har ki  koma wani  aiki.
ni kaina wlh yanzu banaso komarwaki .
dan hk bbu inda zaki ki zauna kema 'cikin yan'uwanki zan fi samun kwanciyar hankali .
Aunty Salmah tace wlh zanceki  gaskiya ne mama  Amman kubari baban  yazo tukun nasan da zarar yasanar mata da  abinda ya zartar akanta zata natsu ... ko babu wannan dalilin bazata koma koina ba inji cewar mama .
murmushi takaici nablah tayi tare da cewa Mama kennan Allah Ni dai zan koma wlh  Amman Na da wata uku  zan dawo gabadaya  gareku.
mama dan Allah  kada kice a'a ta karasa mgnr tana marairaice muryar .
uhmmmm mama ta sauke ajiyar zuciya to shikennan Amman kibari babanki yazo kiji me zaice.
Take sukar bar zance suka shiga wata hirar daban .
karfe hudu daidai sai Ga  direban ummi ya dawo daukar nablah Amman nablah ta fita da kanta tace ba yau zata koma ba sai zuwa jibi ko gata. da zai wuce aunty Salma ta bishi Dan ya rage mata hanya .

Da daddare byn sallar isha'i mlm salisu yashigo gidan da sallama a bakinsa hannushi rike da wata  bakar leda yana shiga dogon parlour gidan.
  idanunshi suka sauka kan diyarsa nablah dake sanye da hijab ajikinta wanda tun safe datazo gidan  bataci re ba tana kwakume dashi abinda Yasa ma mama bata mata maganar ta cire  ba sbd tasan tun asali hk take mayar hijabi ce ita  ko bacci zatayi bata cirewa ..

Ahankali mlm salisu yakarasa shigowa ciki  tare da cewa wanake ganin hk kmr nablah agidan nan ?

Nuratu ta tashi da sauri  jikinta  a sanyaye  ta karbi ledar  hannushi ta ajiye a gefe  tana mishi sannu da zuwa .
Bai kulata ba sbd hankalinsa dake kan nablah ..tsam itama  nablah tayi da ranta tare da shan jinin jikinta sbd ganin irin kallon da mahaifin nata ke jifanta dashi .
jikinta a matukar sanyaye ta bude bakinta da kyar gurin cewa sannu da zuwa baba ..

uhmmmm yauwa Yan neman abun duniya da fatan dai kin samo masu yawa ?
Nablah tayi tsit  ta sake sha jinin jikinta ai nasan duk inda kika je zaki dawo , indai nine ubanki ba shegiya bace ke.....
yakarasa mgnr yana nunata da yatsa hannushi  haba haba  baban Salma tun...ke ...nasakaki cikin maganata ? Ya katse mama Yacigaba da mgnrsa .
Da "yata" nabeelah nake mgn ba da saratu ba .
dan hk banason jin bakinki cikin manta .
  ,ai duk da hadin bakinki yaran nan  suke yi duk isakanci da sukaga dama.
basu dauke ni abakin komai ba km wlh duk lalacewata ni nan nine  ubansu dole km akirasu da sunana  sai dai mutun ya gudu bazan fasa mgn ba da cin uwar yarinya tsit kake jin gurin tamkar babu wasu halittu  acikin parlour  ..mlm salisu  yacigaba har ni ubanki zance miki banason abu kice sai kinyi dole .

AUREN SIRRI COMPLETE Where stories live. Discover now