💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Dedicated to
HAUWA A USMAN
(JIDDARH)Page 101
Gabadayansu suka fita Daga dakin atare.
zuciyar ummi da zeenat cike da matsanancin fargaba da tsoron abinda zai biyo byn wata dayan nan da nablah tabasu.. zeenat so tayiwa ummi mgn akan hukuncin da nablah akan baby's .
Amman bakinta Yayi mata nauyi .
takasa cewa komai Sai dai ita azuciyarta taso ne ace ambar mata yaran gabadayansu ba wai aro aka basu da gindaye sharadi ..Byn fitarsu nablah tayi kuka har da ciwon kai akan rayuwar data tsinci kanta ciki .
Me zatacewa iyayenta da danginta akan yaran ?
Wa zata ce Yayi mata cikinsu ? Sosai tayi kuka tamkar ranta zai fita ..
Ita dai duk rintsi tana son ya'yanta km duk tsananin wuya tana tare dasu km zata rayu da abunta domin sune duniyarta itace duniyarsu .
da daddare deeni yashigo dakin ta Dan dago shanyayyun idanunta ta dube shi wallahi Sai taga duk ya rame mata Yayi Dan wuya , yaja stood ya zauna yana facing dinta idanunshi akanta tayi saurin yin kasa da kanta . muryarsa a raunane.yace me Dame kike so game da suna ?
ta sake dago shanyayyun idanunta ta dubeshi dasu tana maimaita abinda yace a cikin ranta muryarta a sarke tace ni Ina ruwana da wani suna ?
Nifa babbar sunana kugama abinda zakuyi da yarana Ku dawo min da abina nakama gabana .Ya kamo hannuta 'cikin nashi yasoma murzawa yana kallonta agalabaice kana yace Karki damu kanki Ai za a dawo miki dasu .
Amman kafin wannan lokaci Dan girma Allah ki saki ranki sosai kin dinga ci abinci kina basu nono sosai suna Sha . Yakarasa mgnr da duk kinbi kin tada hankalinki sbd yaran nan.
,uhmmmm dole ne naga kmr ana son a farmakeni akansu ne km mgnr bada nono Ai ko bakace ba dole nabasu idan ma banbasu me zanyi dashi?
numfashinsa ya sauke da kyar yana cigaba da kallonta ya km damko dayan hannuta 'cikin nashi yana murzawa ahankali ahankali yana kallonta surar jikinta nablah yakira sunanta ta kalleshi ta sauke idanunta 'cikin nashi .take gaban dukkansu ya buga da karfi .
wai bakya jin komai a game dani ne?
ya fadi hk muryarsa cike da fargaban abinda zatace .
Sai data tsuke tsukaken bakinta hade da lumshe idanunta sannan tace me kake tunanin zanji a game da kai ?
Wani abu makamancin felling akaina ko shaukin kaunata ......... Yayi mgnr yana matse hannuta sosai 'cikin nashi.ta girgiza masa kanta
uhmmmm Gsky ni bana jin wani abu makamancin hk a game da kai .
Sai dai idan Kai ne ke jin hk agame dani .
Yayi saurin lumshe rikitattun idanunshi na 2 second kana ya bude fess yana kallonta tabbas abinda ta fada masa ba gsky bane .
idan dai har shi yana jin wani abu akanta yasan dole ne itama takasance hk ..Ya Mike yakarasa gadon da bbys dinsa ke kwance suna bacci ya sumbacesu daya byn daya Amman ya dade akan bby girl dinsa yana kallonta yana jin kaunar yarinya Na sake huda zuciyarsa komai nata irinn Na nablah ne sak.
bbu abinda ta dauko nashi Sai hasken fata koda ya dawo gurin nablah har tayi shirin bacci .
ta Dan dube shi tace kazo ka wuce bacci nake ji zan kulle kofa uhmmmm babudamuwa kina iya kullewa kawai Dan nima anan zan kwanta .Bangane anan zaka kwana ba ? Tayi masa tmbyr a Dan hassale .
Bai ce daita komai ba ya nema guri can karshen gado ya kwanta .
Yana runtse idanushi .
tazo inda yake kwance ta tsaya akanshi .. please kazo ka bar dakin nan .
Nifa wlh bana son kebencewana da kai alhalin Kai ba muharramina bane.
fizgota taji yayi ahankali bisa kirjinsa ya rungume tsam yana sakin numafashi .
kiyi baccinki anan bbu abinda zan miki .
Muryarta a matukar tsorace tace gsky ni a'a .
ada can baya banyi komai dake ba Sai yanzu ..kina jego
Ta bude baki kennan zata sake yin mgn ya hade bakinsu guri daya yana girgiza mata kanshi da lumshe rikitattun idanunshi masu kashe mata sansar jikinta.
Dolenta tayi shr ta lafe a fadadden kirjinshi tana fidda numfashi sama sama .

YOU ARE READING
AUREN SIRRI COMPLETE
Mystery / ThrillerMatar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan