🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SOORAJ!!!**Written By*
Phatymasardauna*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈Kainuwa 抖阴社区rs Association*
_{United we stand and succeed;our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation**WATTPAD*
fatymasardauna#romance
*Chapter 26*Hanunta tasa da sauri ta goge hawayen daya sauƙo mata akan ƙuncinta, kitchine ta koma ta tare da cigaba da wanke wankenta......
RAJ
Tsaye yake agaban shower ruwa na dukan jikinsa, hannayensa duka biyu ya sanya ya dafe jikin bango, idanuwansa wanda suka sha ruwa sukayi jajur ya buɗe tare da furzar da ruwan dake bakinsa. Maganganun Abba gaba ɗaya sun gama dagula masa lissafi, ko tantama bayayi koda sun nemo zaɓinsu sun aura masa awannan karonma bazai iya jure zama da mace ba, dole zai saketa, sannan kuma dole ne zasuyi fushi dashi, ayanzu kam baya tunanin zai sake yarda alaƙa ba masa nauyin wata ƴa mace akansa, koda sau ɗayane yanason iyayenshi su fahimcesa amma kuma hakan ya gagara, kashe shower'n yayi tare da jawo towel ya ɗaura akan weast ɗinsa, baidamu da yanda jikinsa ke ɗigan ruwa ba ya buɗe ƙofar bathroom ɗin ya fito, idan yace zai iya baje damuwowin dake ranshi to tabbas ƙwaƙwalwa da zuciyarsa bazasu iya ɗauka ba, kaya ya sanya ajikinsa tare da ɗaukan car key ɗinsa yafice daga cikin ɗakin, direct compound ɗin gidan ya nufa, wata baƙar 4matic ya buɗe yashiga tare dayi mata key, tun mai gadi baigama wangale gate ɗin da kyauba ya cilla hancin motarsa waje.Tafiya yake amma gaba ɗaya hankali da tunaninsa suna wani waje daban, ababban ƙofar asibitin yayi parking, yau bakamar ko yaushe ba, don bai shigar da motar tasa ciki ba kamar yanda ya saba.
Direct office ɗin Dr.Yunus ya nufa, yana knocking aka bashi izinin shigowa, kujera yaja ya zauna tare da miƙawa Dr.Yunus hannu sukayi musabaha, cike da fari'a Dr.Yunus yace. "Yajikinnaka ina fata dai ankama waƴanda suka aikata laifin?"
"Dasauƙi!" Sooraj yafaɗa aɗan gajarce kasancewar bayason zancen yayi tsawo.
Murmushi Dr.Yunus yayi domin sarai yasan halin Sooraj sai mutum ya shekara yana masa magana baitanka ba.
Gyara zama Dr. Yunus ya sakeyi tare da cewa "Result ɗinka yana ajiye tun after 1 week" Wata ƴar drawer dake jikin table Dr.Yunus ya jawo tare da zaro wata farar envelope.
Miƙawa Sooraj yayi tare da cewa "Komai yananan daidai, nayi duk wani bincikena dazanyi Sooraj amma gaskia bangano wata sabuwar matsala ba, magungunan dana baka acan baya sune kawai zakana sha har abubuwa su daidaita!" Dr.Yunus yafaɗi haka cike dason kwantar da hankalin Sooraj.Wani murmushin gefen baki wanda yafi kuka ciwo Sooraj yayi, shikaɗai yasan wani irin zafi zuciyarsa keyi masa awannan lokacin, karɓan takardan kawai yayi tare da sake bawa Dr. Yunus hanu sukayi musabaha, daganan yafice daga cikin office ɗin, wani irin kallon tausayi Dr.Yunus keyiwa Sooraj, sosai matsalan Sooraj ɗin ke ɗaure masa kai, iya binciken duniya sunyi shida abokan aikinsa amma sam su basu iya gano matsalan Sooraj ba, hasalima komai nasa lafiya lau yake bashi da wata tawaya a halittar jikinsa. .
Tunda yafito daga cikin office ɗin Dr.Yunus yake ganin duhu a idanuwansa, cikin cijewa ya ƙarasa wajen da motarsa take, yana shiga ya kifa kansa ajikin steering motar tare da fesar da wani breath me ɗumi, aƙalla yaɗauki kusan mintuna 9 ahaka batare dako motsi yayi ba, gaba ɗaya tunaninsa ya tsaya cak.
Da ƙyar ya iya ɗago kansa, idanuwansa tamkar jan garwashin wuta haka suka koma, Envelope ɗin da Dr.Yunus ya basa ya buɗe, tare da zaro wata ƴar farar takarda dake ciki, ahankali ya warwareta tare da sauƙe idanunsa akan rubutun dake cikin takardan . Yana gama karanta abun dake cikinta ya duƙunƙuneta tare da rumtse idanunsa da ƙarfi. Laɓɓan bakinsa yaɗan ciza tare da ɗauko wata lighter ya kunna, takardan yakawo jikin lighter'n take ta kama da wuta, sauƙe glass ɗin motar yayi ƙasa tare da cilla takardan waje, take takardan ta ƙone ƙurmus, key yayiwa motarshi tare da cillata kan titi yabar wajen....

YOU ARE READING
SOORAJ !!! (completed)
RomanceZanen ?addaransa yana cikin zuciyarta, kamar yanda zanen nata ?addan ke cikin tasa zuciyar. Idan zuciyoyi suka ha?e waje guda akan samu wata irin zazzafan ?auna. Ako da yaushe jinsa yake kamar wani ba?on halitta, RAUNI DAMUWA sune abun da sukayi tas...