抖阴社区

Chapter 32

12.2K 1K 99
                                        

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

         *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

        *WATTPAD*
  @fatymasardauna

#romance

        *Chapter 32*

Cikin nutsuwa yake takunsa, tuni Zieyaderh ta koma bayan Pharouk ta ɓoye, rumtse idanunta tayi ƙam cike da fargaba.  Ƙamshin turarensa da yacika hancinta ne  yasanya jikinta ya soma  rawa, saboda tasan zuwa yanzu yana gab dasu.    Sam bai kallesuba balle yasa aransa cewa  da gaske mutanene awajen, kansa tsaye ya wuce.

Aƙalla taɗauki kusan 5 minute ahaka, idanunta a rufe suke, jin shiru bataji motsin kowa ba   yasanya tasoma buɗe idanunta ahankali,  da beuty face ɗinsa tasomayin arba yayinda ya kafeta da sexy eyes ɗinsa,  waro idanunta waje tayi tare da ɗanja da baya tashiga waige waige.

Murmushin daya bayyana dimples ɗinsa yayi, tare da  ɗan kashe mata idanunsa ɗaya.              
"Tsoron me kikeyi haka? ba Brother ɗinki bane?"

Kanta ta sunkuyar ƙasa tare da sauƙe ajiyar zuciya,  duk da bata ganshi awajenba amma amatuƙar tsorace take domin batasan wani hukunci bane zai biyo baya.

"Meyasa kikejin tsoronsa? Ya hanaki kula kowa ne? Waye shi awajenki? Please tell me karkimin ƙarya!"    yafaɗi haka yana me gyara tsayuwarsa tare da kafeta da idanunsa....

Sallama ɗauke aƙasan maƙoshinsa yashiga cikin falon, kai tsaye ɗakinsa ya nufa.

"SOORAJ!" Ummu dake zaune acikin falon taƙira sunanshi. 

Cak ya tsaya da tafiyan, ahankali ya ɗan juyo ya kalleta.

Fuskarta babu alaman wasa batare da ta kalleshi ba tace "Badai ka ɗauki maganganun da Abbanka yayi maka amatsayin wasa ba?"

Shiru yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa, baijin zai iya furta wata kalma awannan lokacin.

Sanin halinsa yasanya Ummu cigaba da cewa. "Kashiga hankalinka Sooraj, yakamata ace kasan mekakeyi, sai yaushene zaka fuskanci cewa ka girma? sai yaushe ne zaka nemawa kanka mutumci da daraja tahanyar yin aure? Ashe kafiso koda yaushe muta faɗa muna nanatawa duk akanka kai kaɗai? Idan kasake mahaifinka yayi mummunan fushi dakai to wallahi ba zakaga da kyau ba, sannan kuma gobe Almustapha zai dawo  ka tura mota a ɗaukosa!" Ummu tafaɗi maganganun fuskarta babu alaman wasa.

Kansa kawai ya jinjina alaman yaji, ko 1 second baiƙara ba ya juya ya shige ɗakinsa.

Da kallo Ummu tabisa, tarasa hali irin na sooraj wani kalan alfano gareshi,  ita tahaifesa amma batasan a ina yasamo wannan miskilancin nasa ba, sam itakam ba haka take ba.

Yana shiga cikin ɗakin ya murzawa ƙofarsa key,  kayan jikinsa ya shiga ragewa, towel ya ɗaura  ya shige bathroom, ruwa ya sakarwa kansa tare da sanya hannunsa na dama ya dafe bango,  lumshe kyawawan idanunsa yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, kansa ya ɗaga sama ruwa ya shiga dukan fuskarsa, saida numfashinsa yasoma barazanan ɗaukewa sannan ya sauƙar da kansa ƙasa, numfashi yashiga fitarwa akai akai, yana mejin zuciyarsa na bugawa da ƙarfi. 

Ƙanƙance idanunsa yayi tare da lumshesu alokaci guda. "Zieyaderh!!" yaƙira sunanta in a cool voice ɗinsa.  

Kanta ta ɗago tare da  ɗan satan kallonsa,  cikin muryarta me sanyi tace. "Na'am!"

"Inasonki!" Yafaɗa asanyaye yana me karyar da kansa gefe.

Kanta tajinjina tare da ɗan sakin murmushi, ƴan siraran laɓɓanta dake motsawa ahankali ya kalla.
Da alama maganace abakinta amma tanajin nauyin furtawa.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now