抖阴社区

Chapter 47

18.2K 1.5K 348
                                        

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ !!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*WATTPAD*
@fatymasardauna
#Destiny.

*(Wannan fejin gabaki ɗayansa na sadaukar dashi agareki.
My Aunty, AISHA ALI GARKUWA. Allah Yaƙara miki lafiya da nisan kwana, Ameen.)*

*Chapter 47*

Hannunsa ya ɗaura adaidai tsakiyar fatar bayanta dake shinning, jin sauƙan hannu ajikinta yasanya ta sakin kwalban turaren humran dake hannunta, yayinda tayi saurin juyowa atsananin tsorace, hartakai ga ƙirjinsu sun samu haɗewa waje guda,
cikin mamakin ganinsa daf da ita ta ajiye idanunta akan faffaɗan chest ɗinsa, saboda bazata iya juran kallon cikin fitinannun idanunsa ba.
Hannunsa dake kan naked skin ɗinta, ya sanya tare da ɗan jan bathrobe ɗin yayi sama, inda yakawoshi harkan kafaɗunta, ahankali ya jawota gab dashi, cikin nutsuwa ya ɗaura hannayensa akan igiyoyin da zasu haɗe bathrobe ɗin su sanya ya kama jikinta, ahankali ya haɗo igiyan tare da sanya hannunsa yasoma ƙoƙarin ɗaure mata igiyoyin akan lafaffen cikinta, kokaɗan bai bari idanunsa sun sauƙa akan ƙirjinta dake aɗan buɗe ba, fuskarta kawai yake kallo, yayinda ita kuma ta rufe kyawawan idanunta, wanda samansu ke ɗauke da zara zaran eye lashes, cikin son zame hannunsa daga jikinta, batare daya sani ba ƴan yatsunsa biyu suka gogi kan nipples ɗinta, wani irin yaaarrr yaji ajikinsa, wanda koda wasa baitaɓa jin kwatankwacin hakan ba.
Ita kuwa Zieyaderh rumtse idanunta tayi da ƙarfi, tare dayin ƙasa da kanta, yayinda wani irin kunyaya rufeta.
Ahankali ya ɗauke hannunsa daga jikinta, tare da ɗan matsawa, cikin takunsa mai ɗuke da nutsuwa ya nufi hanayar bathroom, tanajin rufewar ƙofar toilet ɗin tasaki wata ƙatuwar ajiyar zuciya, tsikar jikintane ke tashi, yayinda gefe guda kuwa taji wani irin sabon abu na baƙuntan gaba ɗaya gaɓɓan jikinta, cikin jin kunyan abun daya faru, taƙarasa gaban ƙaton sif ɗinsa wanda aka jere mata kayanta daga ɗayan ɓangaren, wata dark green ɗin doguwar riga mai faffaɗan wuya ta zaro, cikin sauri sauri ta zura rigar ajinka.

Yanashiga cikin toilet ɗin yasoma ɓalle aninayen gaban rigarsa, cikin abunda aka aje a toilet ɗin musamman don ajiye kaya, ya ajiye rigarsa, makunnin shower ya kunna tare da tsayawa ruwa na dukan murɗaɗɗiyar surar jikinsa, lumshe idanunsa yayi tare da sanya hannu ya dafe jikin bango, tunowa da yanda yaji ajikinsa ɗazun ne, yasanyashi sake lumshe idanunsa,
tunowa da haka yasan yashi sake jin wani sabon abu ya tsarga masa tamkar awannan lokacin abun ya faru, cikin yanayi nason ƙaryata kansa da abun dayakeji, yaɗan soma jijjiga kansa, sam bayason zuciyarsa ta yaudaresa, tabbas yasan komai zaiji ayanzu to sharri da kuma yaudara ne irinta zuciya, koma mene bazai raɓa zama gaskiya ba.
Yajima sosai atsaye ruwa na dukan jikinsa, har saida idanunsa suka sanja kala daga farare zuwa launin ja, kafun ya kashe shower'n,
towel ɗin daya tsaya iyaka guiwarsa ya ɗaura, jikinsa na ɗigan ruwa haka ya murɗa handle ɗin ƙofar ya fito.
Jin motsin fitowarsa yasanya Zaieyaderh komawa kan gado da sauri ta kwanta, tana me dafe saman mararta wanda takejinsa kamar akumbure, gaba ɗaya kwananan batajin daɗi ita kanta batasan meke damunta ba, takan daiji mararta na yawan murɗawa, yayinda takejin ƙasan marartata acike.

ƙarasawa gaban mirror' yayi aƙagauce ya shafa body lotion,tare da body spray ɗinsa mai daɗin ƙamshi, wani blue crazy jeans tare da white t-shirt,
da kuma blue facing cap ya sanya, sosai yayi kyau ya fito acikakken handasome guy ɗinsa, makullin motarsa ya ɗauka batare daya dubi inda take ba yasakai yafice daga cikin ɗakin.
Jin motsin ficewar sa daga cikin ɗakin, yasanyata sake duƙunƙunewa waje ɗaya tare da lumshe idanunta, ahankali sabon mood ɗin da ta samu kanta aciki ke ratsata, yayinda yake ƙara shiga jikinta yana samun wajen zama, sannu ahankali ya mamaye gaba ɗaya jikinta, yayinda yasanya idanunta rufewa, tabbas ita awajenta hakan baƙon yanayi ne, kuwa sam batasan da wani irin dan batasan da wani suna zata ƙirasa ba, tunani ne kala kala acikin rai da zuciyarta, haka tayita juyi har saida aka ƙira sallan magriba, tashi daga kwancen tayi, tare da wucewa bathroom ta ɗauro alwala.

SOORAJ !!! (completed)Where stories live. Discover now