抖阴社区

?8

195 4 0
                                        


💝🌸HARAMTACCIYAR ALAƘA🌸💝

*Written by Fateemah MG

               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ
ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)

🌸Page 8

Sae can gurin ƙarfe biyu na dare Zaynoora ta farka tana jin wani kalan mahaukacin yunwa na ɗibarta, da kyar ta miƙe ta zauna daga kwancan da take dan gaba ɗaya wani special kasala take ji, tun lokacin da Ya Anwar ya hura mata iska a kunni ta fara jin wani da ita kanta bata san meye shi ba. Daga baya kuma ya fara kissing ɗinta a wuya nan fa ya kwance mata notunan kanta, har yanzu ji take kamar lips ɗinsa na kan wuyanta dan har tsikar jikinta take ji suna tashi, hannunta takai ta shafa wuyan nata kafin ta miƙe tsaye ta fara zare straight gown ɗin jikinta, ɗazu ka sa saka kayan bacci tayi dan da kyar ta kammala sallah ma, gaba ɗaya tunanin Ya Anwar da abunda yyi mata ɗazu ne yyi ta yi mata yawo akai, tana gamawa ta shige cikin bathroom sae cikin bathtub, ta daɗe a ciki tana gurze jikinta dan ji take har yanzu kamar da lips ɗinsa kan wuyanta, har sae da skin ɗin wuyanta ya fara zafi ta ajiye sponge ɗin ta ɗauraye jikinta ta fice ɗaure da towel a jikinta. Mai ta shafa kafin ta ciro kayan baccinta gown iyakarsa gwiwa mae laushi sosai, tana saka hula ta zauna akan gado, sae yanzu ta fara tunanin Ya Irfaan ko mey zaeyi mata oho tana cikin tunanin nan cikinta ya murɗa yana neman ɗauki, wutan gidan duka a kashe suke hakan yasa ta ɗauki wayarta ta kunna haske ta fice daga ɗakinta cikin sanɗa zuwa kitchen ɗin gidan. Irfaan ne yyi zaune a parlournsa kansa haɗe da gwiwansa, shi ya kasa gane me yake faruwa dan tabbas yau ya lura da cewar kishin Zaynoora yake yi kuma ba'a matsayin ƙanwarsa ba, a iyakacin saninsa Zaynoora ƙanwarsa ce kuma jini ne ya haɗasu dan mahaifi da mahaifiyarsu ɗaya. Ɗazu da kyar ya iya controlling kansa amma da za'a barshi da sae yyi wa Anwar jini da majina, dan idan har cikin zuciyarsa yake kishin ace wani ya kulata ko ya taɓa ta hakan yasa yake taka tsantsan sosai amma duk da haka shine Anwar zae lallaɓo ya son ya danneta a gidansu bbu kunya bare tsoron Allah, sosai ran Irfaan ke sake ɓaci idan ya tuna yanda yaga Anwar ya ɗan kwanto jikin Zaynoora tana kissing kunnenta. Tsaki yyi tare da miƙewa tsaye, bae ɓata lokaci ba yyi hanyar kitchen dan haɗa tea da ya saba sha da dare dan yana fama da insomnia kuma ya daɗe dashi sosai, kullum baya iya bacci har sae yasha magani amma kasancewarsa likita yasan side effects ɗin amfani da magani kullum haka yasa yake shan herbal tea da zae riƙa ingizashi kafin ya samu baccin.

Yana shiga cikin kitchen ɗin ya tarar da Noor a tsaye gaban cooker tana dafa Noodles, murya can ƙasa yace, "Ke!" Duk da a hankali yyi maganan ba shi ya hanata tsorata ba, a razane ta juyo idanu a waje tsabar tsoro gashi har ta buɗe baki zata kurma ihu, fusgota yyi ta faɗa jikinsa kafin yasa hannunsa ya rufe mata baki tsam, sae daga baya taji ƙamshin turaren Yaya Irfaan hakan yasa ya ta saki jikinta, ɗan faɗowa jikinsa da tayi sae ji yyi wani abu na tsikarin dukkan jikinsa kamar sa allura hakan yasa ya tureta, tana gyara tsayuwarta tace, "Yaya wallahi har ka tsorata ni!" Wutan kitchen ɗin ta ƙarasa ta kunna tunda wayarta ta faɗi ƙasa kuma bata kawo ba, tana kunna wutan ta duƙa ta ɗauki wayarta ta kunna amma sae ta ƙi ta kawo, turo baki gaba tayi cikin shagwaɓa tace, "Yaya wayata taƙi kawowa!" Sae a lokacin ta ɗago kanta tace, "Yaya ka lalatamun wa.." bata ƙarasa ba idanunta suka sauka akan murɗaɗɗiyar ƙirjinsa, wani kunya taji hakan yasa tayi saurin ɗauke kanta nan shima ya juya jin wani yanayi na neman shiga tsakaninsu, bae ko ƙara minti ɗaya ba yyi tafiyarsa dan ya ma manta mae ya kawo shi cikin kitchen ɗin, yana shiga part ɗinsa ya wuce bedroom, akan gado ya baje yana sauke ajiyar zuciya, wanne kalan al'amari ne haka yake neman shiga tsakaninsu da gani sheɗan ne hakan yasa ya shige toilet ya ɗauro alwala, jallabiya ya zura kafin ya tayar da sallah yana neman mafita a gurin Allah dan wannan abu ya fara neman fin ƙarfinsa.

Washe gari da safe ya fito cikin shirinsa na gurin aiki amma sae kusan tara na safiya ya fito, zuwa lokacin Aysha ta wuce school already, yana fitowa ya tarar da Zaynoora tana breakfast ita kaɗai, suna haɗa ido sau ɗaya yyi saurin ɗauke idanunsa, yana sake jin wani yanayi na rufe dukkan jikinsa itakuma kunyansa ne ma ya kamata, da kyar tace, "Yaya ina kwana!" Da kyar dae ya amsa mata gaisuwar a dake nan dae tayi serving ɗinsa ta koma ta zauna tana cin nata abincin, haka dae ya gama kowa yana wani ɗauke kansa, yana gamawa ya miƙe dama ta saba tana kai masa jakanshi mota daga time zuwa time, ba tareda tayi wani tunani ba ta zagayo ta ɗauki jakan nasa ta bishi a baya, duk a kasalance yake jin kansa amma babu yanda zaiyi zuwa aiki ya zamo masa dole, yana isa parking lot ya shige cikin motarsa, hannu ya miƙo mata ta miƙa masa jakansa, murmushi tayi tace, "Yaya sae ka dawo!" Tsintar kansa da kasa ɗauke idanunsa daga kanta yyi, wannan murmushin daya ƙawata fuskarta ga dimples a manyan kumatun ƙara sauke masa kasala suka yi gagarumi. Da kyar ya kwashe idanunsa daga kanta, miƙa masa jakan tayi nan hannunta suka shafi nashi, wani kalan shocking yaji hakan yasa yyi saurin zare hannunsa daga nata, kai shi kansa yyi mamaki mae haka yake nufi, sae a lokacin ya lura kwata kwata ashe bae yi mata komai ba, bata ankara ba sae ji tayi ya kamo kunnenta ɗaya ya murɗe, buɗe baki tayi zatayi ƙara amma ya sa ɗayan hannunsa ya rufe mata baki, ganin bbu yanda zata kwaci kanta sae ta faɗa kansa gaba ɗaya a cikin kujerar motar tasa, wata spark yaji daidai lokacin da ta haɗa jikinta da nashi kamar an jona masa lantarki. Jin wani yanayi na neman lulluɓeshi yasa shi sakin kunnenta nata nan ta ɗago idanunta da suka cika da hawaye, ɗaure fuska yyi yace, "Wato abunda kika zama knn ko? Har a parlour zaki zauna da wani ƙato yana taɓa miki jiki ko a jikinki ko?" Hawayen ne suka fara zuba tace, "Wallah Yaaya Irfaan ba haka bane.." wani kallon banza yyi mata yace, "Ni dae nayi ƙoƙarin yi miki tarbiyyah zuwa abunda kowa zaeyi alfahari dake cikin al'umma, banyi expecting haka daga gareki ba!" Hawayen ta share tace, "Yaaya wallahi.." rigarsa ta kamo tana son yi masa bayani, fusge rigarsa yyi ya rufe ƙofar motarsa ya taka motar ya bar gidan. A gurin ta durƙushe tana jin takaicin kanta da kanta, ta bawa Yayanta kunya da kuma kanta ahaka har take jin daɗin abunda Ya Anwar yyi mata, ji tayi wani tsanar kanta na ratsa zuciyarta, tayi abun kunyan0ⁿ da ko kare baze kalleta ba dan a tarbiyyah gidan Commissioner ƙarshe ne. Sosai take kuka daga ƙasar zuciyarta amma a haka ta miƙe ta wuce cikin gida, a parlour ta tarar da Aunty da Salma a parlour. Zaynoora da Salma suna shiri amma yanzu Salma sae ta fara jin haushin Zaynoora ganin yanda Irfaan ke haba haba da ita sosai abun har yana wuce misali. Dariya Salma ta kwashe dashi ganin Zaynoora na kuka, bayan ta shige ɗaki Aunty tace, "Ko meya same ta oho!" Taɓe baki Salma tayi tace, "Koma meye Allah Ya ƙara, ita ta sani ai!"

Noor na shiga ɗaki ta baje a ɗaki tana kuka mae shiga rai, jan hanci tayi jin wani kwaɗayi na shiga ranta, share hawayen tayi ta buɗe school bag ɗinta ta fara dube dube, nan ta samo wasu chocolates guda biyu, hawaye ne a idanunta amma haka ta fara murmushi. Jan hanci ta sake yi kafin ta ɓare ledar ta fara turawa a baki tana taunewa, jin yadda suke narkewa a bakinta yasa ta share hawayen gaba ɗaya ta mayar da hankali ga cin kayanta. Bayan ta gama ne ta zauna akan gado tana rungume da pillow in banda tunani bbu abunda take yi, tun jiya da taga ƙirjin Yaaya Irfaan sae ta riƙa jin wani abu da ita kanta bata san meye ba, gashi ta lura da yanda yake kallonta ba kamar yadda yake kallon kowa ba, idanunsa idan yana kallonta cike suke da ƙauna da wani abu da bata san meye shi ba. Tasan Yaaya Irfaan yayanta ne na jini amma bata gane wannan abun ba haka, zata tambayi Raudah anjima idan zasu tafi islamiya.

Zaune Irfaan yyi cikin office ɗinsa ya kasa yin komai tun ɗazu banda tunanin Noor bbu abunda yake yi, shi kansa abun har ya fara bashi takaici nan aka yi knocking office ɗinsa, kansa a ƙasa yace cikin cool voice ɗinsa, "Come in!" Jin an shigo kuma takon namiji sae ya ja aji kafin ya ɗaga kai, tun shigowa da akayi ya kawo wani ne kuma bayan ya ɗaga kansa kuwa ya tabbatar, ta ke yaji ransa na wani ƙuna kamar ana tafasa masa zuciya.

????????????? ?????Where stories live. Discover now