抖阴社区

?30

142 3 1
                                        

💝🌸HARAMTACCIYAR ALAƘA🌸💝

*Written by Fateemah MG

               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ
ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)

🌸Page 30

Ko wata wata bae yi ba ya kamo hannun Zaynoora suka nufi bedroom ɗin Aysha amma basu tarar da ita ba hakan yasa suka nufi babban parlourn gidan saboda yasan baza ta wuce can ba tunda yaga yanzu ta fara kusanci da su Aunty da Salma sosai. Kallo Aysha, Salma da Aunty suka bi Irfaan dashi ganin yadda ya kamo hannun Zaynoora kamar wata ƙaramar yarinya, ganin ransa a ɓace yasa Aysha haɗiye maganar da yake a bakinta, gaba ɗaya idanunsa rufewa sukayi saboda tsabar ɓacin rai, suna ƙarasawa cikin parlourn ya kalli Aysha yace, "Aysha, what the hell is the meaning of what you're doing huh?" Zare idanu Aysha tayi jiki ya raina fata a tsorace ganin yadda ya canza lokaci ɗaya, murya a ƙasa tace, "Yaaya meye nayi kuma?" Rage girman idanunsa yyi yace, "Are you asking me abunda kika yi? Oh baki sani ba? Why the hell are you stressing her?" Ɗan jirkita tayi tace, "Ita wace Yaaya?" Saboda tsabar fushi ji yyi kamar ya ɗauke Aysha da mari amma kuma ya samu ya danne zuciyarsa, ajiyar zuciya ya sauke yace, "Noorie! Meysa kike bata aiki kamar wata machine? Idan aiki yyi yawa ayi hiring maid mana amma what the hell is this duk jiba yadda ta rame farraɗ ɗaya!" A fusace Aysha ta miƙe saboda anzo inda take so, dama so take Yaaya yyi magana akan hakan ita kuma ta kunna masa hayaƙi, haɗe fuska tayi tace, "Yaaya nifa ban gane ba wallahi, taya zaka ce wai Noor baza tayi aiki a gidan nan ba? Sauran ne jakunanta da zasu rinƙa yin aiki ita kuma sae dae ta kwanta kawai? Wallahi baza ta saɓu ba kuma maganar rama yanzu ta fara shi" tunda Irfaan yake a rayuwarsa Aysha bata taɓa taɓa ɗaga masa murya ba amma yau ta kai maƙura kuma dole ne ya saita mata tunaninta, ji yyi zuciyarsa tana wani irin tafarfasa hakan yasa shi kanshi bae san lokacin da hannunsa ya sauka akan kumatun Aysha ba, tsabar zafin marin sae da kanta ya karkace zuwa guri ɗaya, ta ɗan jima kanta a ƙasa kafin ta ɗago kanta ta kalleshi, mutanen parlourn kuwa wani kwaƙwaƙwaran motsi bbu wanda yake yinsa ga numfashinsu ma duk a sama shi kuwa banda huci babu abunda yake yi, dafe kumatun tayi kafin tace, "Yaaya ni ka mara saboda Zaynoora?" Ɗage giransa yyi yace, "Yes I slapped you and I'll slap you again indai akan Noor ne!" Ɗan tuye baki tayi haka tace, "Toh ita Noor ɗin sarauniya ce da baza tayi aiki ba? Wace ita da baza tayi aiki ba? Saboda mene zaka ce haka Yaaya wallahi ba adalci bane!" Sake ɗage mata gira yyi kafin ya sake ɗauke ta da wani mari, zuwa yanzu kuwa hawaye ne suka fara zuba daga idanunta, sosai Zaynoora ta tsorata ganin abunda yake faruwa tsakanin Yaaya da Aysha a sanadiyyarta. Wani kallo da taga Aunty da Salma suna yi mata ne yasa tayi saurin ɓoyewa a bayan Ya Irfaan ɗin saboda tsabar tsoro. Miƙewa Aunty tayi tace, "Habaa Likita mana, ya zaka yi haka?" Ko kallin Aunty bae yi ba yacewa Aysha, "Noor tafi sarauniya kuma akan Noor dae sae inda ƙarfi na ya ƙare kina jinaaa!" Shiru kawai Aysha tayi ta ɗan ja da baya tana sake nazarin komai saboda tsabar baƙin ciki da takaici saboda this is the first time Yaaya ya taɓa kai hannunsa kan jikinta, miƙewa Aunty tayi cikin kaɗuwa tace, "Irfaan meye yyi zafi har haka? Saboda Nooratu ne zaka kai hannunka jikin Aysha?" Saurin ɗauke kai yyi kafin yace, "Eh Aunty kuma zanyi abunda yafi haka akan Noor, baku san yadda nake ji akanta bane!" Ɗan shiru Aunty tayi kafin tace, "Tsaya Irfaan, me kake ji ne kam?" Ko kaɗan hankalinsa baya tareda shi a sanda yace, "A raina nake jin Noor, sonta nake ji a raina sosai kamar baku tunani" ɗiff numfashin kusan kowa a ɗakin ya ɗauke dan sun kasa gane me yake faɗa ma dan kusan ba cikin hayyacinsa ya faɗa hakan ba, shi kansa sae bayan da ya faɗa hankalinsa ya dawo jikinsa sae kuma yyi shiru dan jikinsa yyi sanyi sosai. Sae da aka ɗauki kusan 3 minutes kafin Aunty tace, "Mey kake nufi Irfaan? Kace sonta kake yi?" Ɗan sinnar da kai Irfaan yyi kafin ya ɗaga kansa bayan ya tattaro confidence ɗinsa yace, "Eh Aunty sonta nake yi, sonta nake yi kuma aurenta zanyi!" A zabure Aysha ta ɗaga idanunta ta zuba masa idanu shi kuwa ko kallo bae ishe su ba, gyaran murya Aunty tayi tace, "Aurenta zaka yi? Hankalinka ɗaya kuwa ko wani abun ka sha ne?" Murmushi yyi kafin yace, "Eh aurenta zanyi kuma hankali na ɗaya kamar yadda ban sha komai ba, ban taɓa sha ba tunda so karki ce zan sha wani abun a yanzun da na girma!" Ɗagowa Aysha tayi tace, "Yaaya ba tarbiyyar da ka tasar da mu akanta bane, tarbiyya mae kyau cike da ilimin addinin musulinci ka bamu saboda mene zaka ce haka a yanzu bayan kasan haramun ne?" Kallonta kawai yyi kafin yace, "Idan har baki tambayi tarbiyyar da na yi miki ba toh karki fara tambayar abunda nayi yanzu!" Yana faɗan haka ya kama hannun Noor suka wuce part ɗinsa gaba daya, ita kuwa tsoro ne ya kama ta ganin yadda duka matan ke kallonta in a spiteful manner. Suna ƙarasawa cikin parlournsa ta samu guri a kujera ta zauna tana sheƙa kuka kamar wacce aka daka tana faɗin, "Shikenan na shiga uku yanzu ya zanyi da raina?" Guri ya samu ya zauna yana sauke ajiyar zuciya kafin ya kamo hannunta yace, "Noorie look at me!" A hankali ta ɗago daran daran idanunta ta saka a cikin nasa, sosai idanunsa suka koma soft akan ɗazu da kamar idanunsa zasu fitar da wuta, shafa hannunta ya fara a hankali kafin yace, "You trust me right?" Ɗaga masa kai tayi a hankali nan yace, "Ki kwantar da hankalinki, I'll take care of everything!" Wasu hawayen ne suka sauko daga idanunta kafin taja hanci tace, "Yaaya fah yanzu zasu tsane ni sosai, ni tsoro nake ji" hannunsa ya kai ya share mata hawayenta kafin yyi mata murmushi yace, "Kar ki damu kanki saboda su, my love for you will be enough!" Murmushi tayi masa kafin ta ɗan jinginar da kanta da kafaɗarsa. Ɗan juyo da ita yyi ya manna lips ɗinsa akan goshinta, lokaci ɗaya taji wani warm feeling yana karaɗe jikinta daga lower belly ɗinta, murmushi ta mayar masa kafin ta gyara kwanciyar kanta a kafaɗarsa, sun jima sosai a haka kafin yace, "Muje na raka ki room ɗinki kinga bae kamata ki kwanta ba a nan!" Kai ta ɗaga masa nan ya kama hannunta suka fita daga part ɗinsa, Aunty da Salma suna cikin hira sama sama sae ga Irfaan ya fito daga part ɗinsa riƙe da hannun Zaynoora without fear of abunda wasu zasu faɗa akansa, ko kallonsu bae sake yi ba ya raka ta har part ɗinsu. Sae daya tabbatar ta kwanta har ta shiga cikin duvet, ya ja mata duvet ɗin da murmushi a fuskarsa da ta sake ƙawata kyawunsa, murmushin da yyi slipping daga lips ɗinta ne yasa kawai ya duƙa ƙasa kaɗan, quick kiss ya manna mata a lips ɗinta kafin ya gyara tsayuwarsa. Kunya ne ya cikata hakan yasa tayi saurin rufe fuskarta tareda juya masa baya, murmushi mae sauti yyi kafin yace, "Take care!" Yana faɗin haka ya juya ya fice daga ɗakin, idanu Aunty da Salma suka bi Irfaan dashi amma ko kallo basu ishe shi ba, shiri yyi abunsa ya fice ya tafi asibiti tunda akwai VIP patients ɗinsa da zae duba a yau da rana.

Vote☺️🌸

Comment💐💕

And Share!🥹✨️

©️Fateemah MG

????????????? ?????Where stories live. Discover now