💝🌸HARAMTACCIYAR ALAƘA🌸💝
*Written by Fateemah MG
....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ
ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)🌸Page 17
Shiru Wahidah ta zauna a parlour ita kaɗai kamar mayya kowa ya tafi ya barta a zaune, tana cikin zaman ne Aysha ta shigo cikin gida a gajiye da alama daga school take, tana ganin Wahidah ta samu guri ta zauna nan Wahidah ta gaishe da Aysha harda cewa Yaya wanda hakan yyi wa Aysha daɗi ganin yadda Wahidah ke da girmamawa, murmushi Aysha tayi tace, "Ya Ummanki?" Murmushi Wahidah tayi tace, "Umma na gida tana lafiya!" Murmushi Aysha tayi kafin ta taɓe baki tace, "Da wa kika zo?" Tana faɗan hakan kuwa Irfaan ya danno kai cikin parlourn, bakinsa ɗauke da sallama yana ganin Aysha ya ɗauke kansa yace, "Tare dani take, do you have a problem?" Da sauri Aysha ta girgiza kai kafin ta miƙe tace, "Toh ki gaida gida da Umman naki!" Kai Wahidah ta ɗaga mata kuma ta fara kallonta har ta shige part ɗinsu, sae zuba ido takeyi ko Noor zata fito amma shiru, juyawa tayi ta kafe Irfaan da manya manyan fararen idanunta, suna haɗa ido yyi saurin ɗauke kansa yana gudun ta hango soyayyar ƙanwarsa ƙarara a idanunsa.Ɗan tsuke baki yyi yace, "Muje nayi dropping ɗinki kar dare ya yi!" Kai ta ɗaga masa kafin ta bi bayansa har zuwa parking space, sae da ta shiga kafin yyi starting motar suka fita daga gidan kuma har suka isa bbu wanda yyi magana har sae da yyi parking a ƙofar gidansu, murmushi tayi masa kafin ta fita. Har zae taka mota ya bar gurin yaga ta zagayo fuskarta cike da fara'a, murmushin ya mayar mata amma ta dole ce nan ta miƙa masa wayarta tace, "Yaya I want your contact!" Ba musu ya karɓa wayar ya saka mata number and all that while idanunta na kan fuskarshi tana jin sonshi na sake ratsata, ga yanda kyawunsa ke ƙara tafiya da ita, miƙa mata wayar yyi nan tako danna call, bbu wata hayaniya wayarsa ta fara vibration tana kawo wuta nan tayi murmushi tana tsuke baki, bae ƙara ko minti ɗaya ba ya taka motar ya bar gurin inda tayi tsaye yana kallonsa har motar ya ɓace daga sight ɗinta.
Yana isa gida ya shige cikin ɗakinsa yana jin bbu daɗi gashi har wani bugawa zuciyarsa take yi saboda tsabar son ganin Noor, a ɗakinsa yyi zamansa sae dinner ne kawai ya fita amma still bata fito ba, kallon Aysha yyi yace, "Aysha ina Noor?" Ɗan tsuke baki tayi tace, "Tana ɗaki tace mun bata da lafiya!" Sosai ya tsorata da jin hka amma baece komai ba sae ɗaga kai da yyi, sosai Aunty ta zuba masa idanu tana nazarinsa ciki makirci, suna gama cin abinci ya koma ɗakinsa, bedroom ɗinsa ya faɗa ya zare jallabiyar jikinsa sannan ya kife akan gado. Ganin hakan ba mafita bane yasa ya jawo laptop ɗinsa tareda glasses ɗin karatunsa ya fara karatun amma kuma bbu abunda brain ɗinsa take processing, banda tunanin Noor bbu abunda yake yi, ture laptop ɗin gefe yyi ya zura hannunsa cikin gashin gansa fiercely yana jin wani nauyi da zuciyarsa take yi masa, tuno da kiss ɗin da suka yi sharing ranar yyi nan jikinsa ya ɗau rawa kamar an jona masa lantarki, agogon dake manne da bangon ɗakin ya kalla, ganin ten ne har yanzu kuma akwai possibility ɗin cewar idon Aysha a buɗe yasa ya shige cikin bathroom ya watsa ruwan sanyi ko kansa zae yi cooling zuwa lokacin da zae samu yyi slipping zuwa ɗakinta, dole ne ma ya ganta yau yau ɗinnan idan ba haka ba tsab zuciyarsa zata fashe kafin garin Allah ta waye, yana fitowa daga toilet ya sake duba time ganin ten minutes ne kawai ya ƙaru yasa yyi deciding yyi risking ɗin komai, dogon wando kawai ya saka da wata plain white shirt ya fice daga part ɗinsa.
Kasancewar yasan his way round the house yasa yyi slipping zuwa part ɗinsu soundless, a hankali ya taɓa ƙofar ɗakinta kafin ya murɗa doorknob ɗin ya shige, ɗakin cikin dim light yake saboda kashe main switch ɗin wutan da tayi sae bedside lamp da yake a kunne kuma haskensa orange ne ma haka, a kife ya ganta akan gadonta da alamar har yanzu kuka takeyi saboda tana jin sheƙan kukanta, sanye take da kayan bacci na riga da wando masu laushi sosai. Hannunsa ya kai ya taɓa hannunta, da ƙarfinta ta fusge hannunta tace, "Ya Aysha ki kyaleni" sake kai hannunsa yyi zae ɗagota nan ta juyo a fusace tace, "Nace na fasa yin maganar Ya Aysha ko ana dole ne..." tayi niyyar faɗawa Aysha lamarinta da Anwar amma tace tana abu lokacin yanzu kuma taji bazata iya faɗa ba.
