💝🌸HARAMTACCIYAR ALAƘA🌸💝
*Written by Fateemah MG
....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ
ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)🌸Page 19
Ai kasa tashi yyi daga zaunen nan har sae da kowa ya tashi ya barshi shi kaɗai yana cakuɗa abincin dan ya ma kasa cin abincin, gama juyawa yyi ya miƙe ya nufi parlour ya zauna a gefen Mama, kallonta yyi kafin yace, "Mama.." shiru tayi kafin ta juyo a hankali ta zuba masa idanu, kansa a ƙasa yace, "Toh ita wannan yarinyar ina taje ne?" Ɗan zare idanu tayi kafin ta ɗauke kaɗai tace, "Meysa nake ji kamar kana kishi da ƙanwarka?" Wani bugawa zuciyarsa ta fara yi da sauri da sauri nan dae yyi saurin ɗauke kansa kafin Mama ta ɓaro jirginsa, da nauyin baki yace, "A...ah ki..kishi kuma... aah.. kawai dae ...ni nafi so ta gama... sch..school ne kawai" rage girman ido Mama tayi tana kallonsa sosai kafin ta taɓe baki tace, "Toh meysa nake ganin kamar kishin kk yi daita ko auren ne baka so tayi?" Sosa ƙeyarsa ya fara kafin yace, "Aah ni ba haka nake nufi ba!" Kansa ya daɗe a ƙasa yana ɗaga kansa kuma yaga idanun Mama a kafe akansa, saurin ɗauke kansa yyi nan yaji muryarta tace, "Wacce kalar alaƙa ce tsakaninka da Nooratu? Eye Irfaanu?" Saurin ɗago kansa yyi yace, "Maama alaƙa... kuma?... wacce...wacce take tsakanin Yaya da ƙanwarsa mana" taɓe baki tayi tace, "Ka tabbatar?" Ɗaga kansa yyi yace, "Eh Maama ko zargi na kike yi ne?" Saurin girgiza masa kai tayi tace, "Aah, a matsayin Uba kk gareta dan haka ni bance zarginka nake ba Irfaan" kai ya ɗaga mata nan kuma ta ɗauke kanta tace, "Amma kuma tunda ta nuna aure take so mae zae hana kayi mata auren kawai" saurin ɗago kansa a firgice ya kalleta kafin ya sauke kansa ƙasa, miƙewa yyi daga bisani yana shafa gashin kansa yace, "Zan shiga daga ciki, sae da safe Maama" kai kawai ta ɗaga masa nan ya shige cikin ɗakinsa, kwance yyi akan gadonsa yana jin yadda zuciyarsa ke zafi duk idan ya tuna cewar Noorie tana waje tareda wani gardi da bae san ko waye ba, juyi yyi bisa gadonsa yana lumshe ƙananun idanunsa. Kamar ya fita waje ya dubota ko zuciyarsa zata samu salama amma ya tabbatar cewa Mama tana parlour har yanzu hakan yasa kawai yyi luff kan gadonsa yana shafa gashin kansa every now and then.
Irfaan na shiga part ɗinsa ya bar Maama a zaune a parlour tana nazarce nazarcenta a tsanake, ta ɗan jima a zaune sae ga Aunty ta fito daga part ɗinta fuskarta bbu wani annuri sosai ta ƙarasa inda Maama ke zaune ta samu guri ta zaune, kallonta kawai Maama tayi ta ɗauke kai tace, "Sannu Zainabu" Murmushi Aunty tayi tace, "Yawwa Maama dama ina son yin wata magana ce dake!" Juyowa Mama tayi with full concentration tace, "Toh Zainabu ina jinki" ɗan inda inda Aunty ta fara kafin tace, "Ni alaƙar Irfaan ce da Noor naga kamar da ayar tambaya ko baki lura ba?" Taɓe baki Mama tayi tace, "Ayar tambaya kuma? Toh kamar yaya Zainabuu? Me kike nufi kenan" ɗan dariya Aunty tayi kafin tace, "Kalar alaƙar dake tsakaninsu nake magana wallahi baki gansu ba yanda kika san wasu masoya wani lokacin idan suna abu wallahi" Shiru Mama tayi tana kallonta tace, "Zainabuu yanzu dae kice zargin Irfaan kike yi?" Saurin girgiza kai Aunty tayi tace, "Aah ba zarginsa nake yi ba kawai dae na lura da hakan ne" tsaki Mama tayi tace, "Ah gaskiya Zainabu baki yiwa Irfaan adalci ba, wacce alaƙa ce zata kasance tsakaninsu idan bana Yaya da ƙanwa ba?" Shiru Aunty tayi kafin tace, "Zanfi kowa fatan ace haka ya kasance gaskiya, yawwa dama Salma ce ta nuna tana son Irfaan ɗin kuma ta nuna masa haka amma bae ko nuna ya sani ba, shine nace bara na yi miki magana ko da akwai abunda zaki iya yi akai" baki a buɗe Mama ta tsaya tana kallon Aunty kafin tace, "Kinsan me kike faɗa kuwa Zainabuu? Yanzu Irfaan ɗin kike so ki haɗa da Salamatu naga ko karatu bata yi ba" dariyar keta Aunty tayi tace, "Aah tayi har secondary school mana kawai dae bata cigaba bane" taɓe baki Mama tayi tace, "Koma dae meye kawai ki manta da wannan maganar kafin yaji ya ɓata miki rai" kai kawai Aunty ta kaɗa kafin ta miƙe ta nufi part ɗinta ba tareda tayi wa Mama sae da safe ba. Tana isa ta tarar da Salma a ɗakinta tana safa da marwa dan har ta kasa zaune bare tsaye, Aunty na shiga Salma ta ƙarasa kusa da ita tace, "Aunty ya kuka yi da ita?" Taɓe baki Aunty tayi tace, "Wannan mata mae baƙin hali ai nuna mun tayi baze yiwu ba har tana wani cemun baki yi karatu ba" zaune Salma tayi ta ɗaura hannayenta akanta tace, "Shikenan yanzu ni banga amfanin zama na a gidan nan ba idan har Ya Irfaan baze aure ni ba" tsaki Aunty tayi kafin ta juya ta fice daga ɗakin ta bar Salma cikin halin damuwa.
Tsaki Maama tayi a parlour dan sae yanzu maganar Zainabu ya ɓata mata rai wato ma ita ta samu ta aure Alhaji shine har take so ta ƙaƙabawa Irfaan ƙanwarta toh wallahi baze taɓa yiwu ba, tana cikin tunanin nan sae ga Zaynoora ta shigo cikin gidan fuskarta ɗauke da murmushi, kallo ɗaya Mama tayi mata tace, "Har kin shigo?" Ɗaga kai Noor tayi kafin ta zagaya ta zauna a gefen Mama ta wani kwanta kan kafaɗarta a shagwaɓe tace, "Eh na dawo, na daɗe ko?" Dariya Mama tayi kafin tace, "Waye ɗin ne?" Ɗan rufe fuska Noor tayi tace, "Ya Anwar ne fah, abokin Yaya Irfaan ne amma Yaaya baya so" shiru Mama tayi tana murmushi kafin tace, "Shi dae ya sani" tana faɗar haka kuwa wayar Noor ya fara ringing, da sauri tayi picking ta maƙala a kunne tana murmushi, kallonta kawai Maama tayi ta miƙe tace, "Kinga tafiya ta sae da safe" kai kawai ta ɗaga wa Mama tayi waving ɗinta kafin ta juya ta cigaba da waya ita da Anwar, mae yake faɗa mata oho amma abu kaɗan sae ta kwashe da dariya ko tayi ta murmushi ita kaɗai.
Wani juyi Irfaan yyi a kasalance yana jin yadda kansa ke ciwo amma ba sosai ba, yunƙurawa yyi ta tashi zaune a gajiye hannayensa ya ɗaga sama yyi flexing bones ɗinsa kafin ya sauka daga gadon, idanunsa ya sauke akan agogon dake ɗakin ya ga har ƙarfe biyu saura amma ya samu bacci sosai ai, toilet ya nufa ya wanko fuskarsa kafin ya juya ya fice, haka kawai yaji zuciyarsa ta buga da ƙarfi bayan ya tuno da Noor ai ba shiri ya juya ya fice daga ɗakin cikin jallabiyarsa dan ya tabbatar ko ta shigo gida kuma wanne time ta shigo gidan, haka kawai Mama zata ɗaurewa yarinya baya ta lalace ana zaune ƙalau. Ai saboda tsabar hira tayi daɗi yawo Noor ta fara yi a tsakar parlourn ta taɓa wannan ta taɓa wancan, ƙara tajiyo daga part ɗin Yaya Irfaan hakan yasa tayi saurin ɓoye wayarta a bayanta, ai juyawan da zata yi har ya ƙaraso inda take, nan fa jikinta ya fara ɓari saboda tsabar tsoro. Shi kuma ganinta da kayan data fita dashi ɗazu sae ransa ya ɓaci sosai, idanu kawai ta zuba masa tana kallon eyeballs saboda tsabar tsoro, muryarsa a sarƙe yace, "Ina kika je?" Cikin muguwar fargaba tayi masa shiru inda shi kuma shirun nan ba ƙaramin ɓata masa rai yyi ba, rai a ɓace yace, "Dan iskanci ina yi maki magana kinyi shiru ne? Zan kakkarya ki a nan gurin" jiki na rawa tace, "Wallahi tun ɗazu na dawo Yaaya ka tambayi Mama" shiru da yyi sae ji yyi kamar ana, 'hello baby, are you there?' Wani zabura Irfaan yyi da jin maganar nan saboda ba ƙaramin ɓaci ransa yyi ba kuma ga yadda zuciyarsa take yi masa kamar an kunna masa wuta, ganin yana ƙoƙarin kai hannu ya fusgo wayar dake bayanta yasa ta tura masa ƙirji gaba ko hakan zae sa yyi backing off, shi kansa bae ankara ba saboda ya riga ya tura kansa nan dae ya tsinci kansa a wuyanta da ƙirjinsa manne da manyan cherries ɗinta, wani yanayi ya shiga mae kamar an jona masa lantarki tun daga brain ɗinsa har ƙafafunsa. Luff ai yyi a jikinsa jin yadda yake jin laushin jikinta a nasa, shiru tayi masa dan ita duk tsoronta ya ga wayar Anwar a hannunta dan har yanzu daita suke waya. Daga farko dae Anwar yaji kamar muryar Irfaan amma daga baya kuma sae ya tabbatar kuma sae ya kama mamakin abunda ya fito dashi a cikin darennan, ƙarshe dai kawai yyi tsaki ya kashe wayar yana tsoron kar ya tonawa Noor ɗin asiri. Sun ɗauke lokuta sosai a manne da juna, Irfaan dae shiru yyi yana jin yanayin dake mamaye jikinsa ga ƙamshi dake fita a jikinta mae neman fitar dashi cikin hayyacinsa. Har launi idanunsa suka fara chanzawa yana shiga yanayin jin bacci a hankali, sautin tafiya ce ta fara ƙarasowa gurin kuma har aka ƙaraso basu sani ba sae jin muryar Mama suka yi tana cewa, "Su waye nan? Nooratu???" A firgice Irfaan ya janye jikinsa daga jikin Nooratu jin muryar Mama ta karaɗe kwakwalwarsa, kusan a gigice Irfaan ya matsa baya sae ganin Mama yyi tana ƙarasowa gurin, kallonsa Mama tayi tace, "Aah Irfaanu, me kake yi a nan?" Ɗaga kansa yyi kafin ya ɗauke kai yace, "Aah, ruwa zan je sha a kitchen shine...shine..." ɗauke ido tayi tace, "Shine me? Ke kuma me kike yi anan kika maƙale jikin bango?" Wani rau rau Zaynoora tayi da ido kafin tace, "Dama.. dama.." taɓe baki Mama tayi tace, "Maza ki wuce ɗakinki ki kwanta yanzun nan" jiki na rawa Noor ta juya ta wuce ɗakinta, idanu Irfaan ya bi Noor dashi kafin ya ɗaga kai ya kalli Mama, suna haɗa ido sae kunya ta kamashi ai kawai juyawa yyi ya wuce part ɗinsa cikin sarfa. Hannu Mama ta ɗaura a kan ƙugunta tana murmushi, can kusa ta cize hannunta kafin ta ɗaga kai ta tura kanta cikin kitchen ɗin gidan.
‧₊˚ ☁️⋅♡𓂃 ࣪ ִֶָ☾.
Drop your votes!🥳❤️🥂
©️Fateemah MG
