抖阴社区

?29

151 3 1
                                        

💝🌸HARAMTACCIYAR ALAƘA🌸💝

*Written by Fateemah MG

               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ
ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)

🌸Page 29

__________

Har wani sauri Salma takeyi ta ƙarasa cikin kitchen ɗin ta cigaba da abunda ta fara a dinning table, tana shiga kitchen ɗin kuwa bata ankara ba taji an shaƙo wuyanta, ɗiff numfashinta ya fara ƙoƙarin ɗaukewa saboda rashin iskar shaƙa, sae da idanunta suka yi jaaa ya sake ta ganin har ta fara kakari. Rage girman idanunsa yyi tareda fusgarta zuwa can cikin kitchen ɗin so that mutanen dinning baza su ji abunda ke faruwa ba. Suna kai ƙarshen kitchen yyi wurgi da ita nan fa ta zube a ƙasa, rage tsayinsa yyi yace, "Are you stupid? How dare youuu? Nayi maki kama da ƴan iskan mazan da kike tunani ne?" Saurin girgiza kai tayi saboda tayi mugun tsorata dama tana yi masa abunda take yi ne saboda tana tunanin zae bata zuciyarsa idan ta ɓullo masa ta haka amma kuma yanzu ta gane sam ba haka yake ba. Saboda baya son exaggerate maganar da kuma cewar shi ba mae faya son surutu bane sae kawai ya juya ya fice abunsa ba tareda ya sake ce mata komai ba. Ko dinning table ɗin bae kalla ba ya wuce part ɗinsa saboda tsabar takaici daya cika masa rai, shi ko kaɗan bae san meyasa mutane ke tunanin kowa halinsa ɗaya da sauran mutane wanda ko kaɗan ba haka bane.

***
Ko one week ba'a yi ba Aysha ta dawo daga NYSC camp ɗinsu da aka tura ta, ta fita da result mae kyau kamar yadda kowa yake expecting kuma kasancewar ita karatu ta saka a gaba toh babu wani sauriyi da take dashi sae dae idan Allah Ya kawo tunda ta shirya yanzu. Tunda ta dawo taga alaƙar Yaya da Noorie ya ƙara ƙarfi har ya fi na da amma kuma bata damu ba tunda Noor ce auta so she deserves princess treatment daga gurin Yaaya, Salma ma dae ta lura da yanda suke kallon junansu duk lokacin da sukayi clashing a cikin gidan, like duk wanda yasan kallon soyayya toh literally shi suke yiwa junansu ba wai alaƙar ƴan uwan jini ba, tun hakan baya damun Salma har ya fara damunta sosai saboda ta fara ganin Yaya yana yawan zuwa part ɗin su Noor yyi mata sallama kusan kullum kafin yyi bacci kuma sometimes ma ko ma kusan ko yaushe shi yake kaita makaranta yanzu. Ganin ta rasa ma dafa sae ta wuce gurin Auntyn ta ta tsegumta mata ko zata samu sauƙi a ranta amma babu abunda zasu iya yi akan hakan tunda bata shafe su ba. Ranar da yamma haka Salma ta bugi ƙirji ta shiga part ɗinsu Noor, bata wuce ko ina ba sae ɗakin Aysha. Tana isa ta tarar da ita tana danna waya cikin fara'a dae haka, Aysha na ɗagowa ta kalli Salma cikin ɗakinta kuma bata yi mata sallama ba, ɓata rai tayi tace, "Baƙar munafuka meye ya kawo ki ɗakina, uban wa yace ki shigo mun ɗaki da wannan banzan takalmin" ba musu Salma ta cire takalmin kafin ta shigo cikin ɗakin mae kyau ta samu guri jikin gadon ta zauna, ajiyar zuciya ta sauke kafin tace, "Wata magana ce a tafe dani Aysha kawai ki saurare ni" ajiye wayar Aysha tayi tace, "Allah Ya sa naji alkhairi saboda ke kamar maciji kike ganinki ba alkhairi bane" Murmushin yaƙe Salma tayi tace, "Maganar akan Yayanki ne da kuma ƙanwarki, wallahi naga kamar akwai wata alaƙa mae kamar soyayya a tsakaninsu" ai Aysha bata yi wata wata ba ta kwashe Salma da wani mari mae kyau kafin tace, "Idan kika sake buɗe bakinki mae dauɗar masifa kika jefe su da haramtacciyar alaƙa toh kuwa zan iya yi miki koma meye kuma na zauna lafiya" shafa fuskarta Salma tayi kafin tace, "Bawai jifansu nake yi ba, ina so ku saka kunne da idanun basira ki gani da kanki, na barki lafiya" tana faɗan haka ta tashi ta fice daga ɗakin cikin tsabar takaici ko da yake gulma ne ya kaita kuma shi ya jawo mata kyautar mari ma amma kuma bata yi a banza ba tunda tasan Aysha is very curious toh dole zata lura kuma tayi nazarin abun. Salma na fita Aysha ta ɗauki wayarta amma gaba ɗaya tayi loosing interest akan abunda take yi da wayar, Salma ta tasar mata da wani ƙuran zato da ta daɗe tana yi amma kuma ta samu ya lafa bayan ta samu yaƙinin cewa hakan baze taɓa faruwa ba.

Sosai Aysha ta saka wa Noor ido kuma ta lura da kalan kallon da Yaya yake yiwa Noor mae kamar soyayya ƙarara ɗin wanda hakan ba ƙaramin ɓata mata rai yyi ba, ki kaɗan bata so Aunty ko Salma su samu wani abu da zasu rinƙa jefan familyn su dashi amma kuma bbu yadda zata iya da Yaya ai tunda tasan mutum ne mae hankali da tunani amma duk da hakan ranta bae fasa ɓaci ba saboda tana ganin kamar abu ne wanda baze taɓa yiwu ba. Sae da ta karance su tsab na kusan sati ɗaya taga dae gaskiyar maganar Salma ne gashi yanzu bini bini yake zuwa part ɗinsu amma kuma Yayanta ne kuma bata ga fuskar da zata ce zatayi confronting ɗinsa ba hakan yasa ta mayar da duk wani zafin abunda take ji kan Zaynoora. Ah da Aysha ce Noor baza ta riƙa yin aikin gida ko ɗaya ba amma yanzu sae ta fara yawan faɗa, ita dae Noor lokaci ɗaya taga Ya Aysha ta chanza mata duk da tasan tana da zafi amma bata nuna mata sae cikin kwanan nan, ranar wata Saturday gaba ɗaya wuni tayi tana aiki tun daga safe har dare, tana gamawa taji bayanta ya riƙe ga zafi da yake mata, kusan tun da aka haifeta bata taɓa aiki kamar na yau ba hakan yasa ta shige ɗaki tayi ta rusa kuka kamar zata mutu, abunku da mutum mae son jikin bala'i ga kasala kamar mae ciki, tana cikin kukan ne Aysha ta shigo cikin ɗakin, tana jin yanda kukan Noor ke taɓa mata zuciya kuma tana jin tausayinta amma abunda suke ita da Yaya ko kaɗan baya burgeta dan ji takeyi kamar zata haukace idan ta fara nazarin abun, like taya za'a yi siblings from the same parents su fara son junansu ko kuma wani shauƙi ya shiga tsakaninsu, hakan yasa Aysha ɗaukar ɗamarar cewa idan sun kasa raba junansu ne toh ita zata taimaka ta raba su for good. Taɓe baki Aysha tayi tace, "Au kuka kike yi? Toh wallahi kaɗan kika gani, ba kince aure kike so ba toh ai abunda ake yi a can kenan sae ki koya tun daga gida! Aikin banza kawai" har ta juya zata fita Noor tace, "Ya Aysha kawai ki faɗa mun abunda nayi miki da yasa kika tsane ni haka kawai" wasu hawaye ne suka taso wa Aysha taji kamar taje ta rungume ƙanwarta amma kuma ai punishing ɗinta take yi akan abunda take neman fara yi da bata san mara kyau bane. Murmushi Aysha tayi tace, "Ni ba tsanarki nayi ba soyayya ce!" Tana faɗan haka ta juya ta fice daga ɗakin, ko two hours ba'a yi ba sae ga Ya Irfaan ya shigo ɗakin, ganin Noor tana kuka ba ƙaramin tayar masa da hankali yyi ba hakan yasa ya samu guri ya zauna yana kallonta cikin damuwa sosai.

Vote☺️✨️

Comment💐❤️

And Share🙂💕

????????????? ?????Where stories live. Discover now