抖阴社区

?9

173 3 0
                                        


💝🌸HARAMTACCIYAR ALAƘA🌸💝

*Written by Fateemah MG

               ....ᖴᗩTᗴᗴ ᗰᗩᕼ
ᗩᒪᕼᗩᗰᗪᑌᒪIᒪᒪᗩᕼ_(◕‿◕✿)

🌸Page 9

Dr Anwar na ƙarasowa ya zauna a kujera yana kallon Dr Irfaan da ya haɗe rai kamar baƙin hadari, ajiyar zuciya Anwar ya sauke yace, "Irfaan da gaske fah nake, wallahi ina son Noor!" Rai a ɓace Irfaan yace, "Dallah malam dakata! Kai ko kunya baka ji ba!" Wani kalar tafarfasa zuciyar Irfaan take hakan yasa jijiyoyin kansa da na hannayensa duk suka fito, ɓata rai yyi ya tashi daga kujerarsa, hannayensa duk sae rawa suke yi hakan yasa ya zura su cikin aljihunsa ya ƙarasa gaban windown office ɗinsa dake kallon view ɗin cikin gari da gaban asibitin gaba ɗaya. Jin amsar da Anwar ya bayar ba ƙaramin ɓata masa rai yyi ba, "Kunyan me, dan ina son Noor sae na ji kunya!" Shiru Irfaan yyi yana dunƙule hannayensa dake ƙoƙarin yi katoɓara, shiru yyi wa Anwar amma shi baeyi shiru ba sae cigaba ma da yyi, "Dan na nuna mata yadda nake sonta shine abun kunya?" Wani zabura Irfaan yyi cikin zafin nama aikuwa ya wanke Anwar da mari yana buɗe masa idanu kafin ya kamo collar rigar Anwar yace, "Abun kunya? Shin har kana da bakin magana? Are that shameless Anwar? You're talking about my damn sister and if you try anything funny I'll fucking deal with you!" Sakin Anwar yyi sannan ya hankaɗa shi gefe yana maida numfashi, dariya Anwar yyi dan shi ko kaɗan abunda Irfaan yyi masa da wanda zaeyi nan gaba baze dameshi ba dan ya ɗauki alwashin mallakar Noor. Tunda yyi ido huɗu da ita yaji ta tafi dashi gaba ɗaya, gata da shagwaɓa ga ta ƴar tulluƙa mae son jiki, shi haka yake son matarsa ta kasance tana manne masa gashi ya samu kyakkyawa kuwa jiki duk madara. Murmushi Anwar yyi yace, "Noor da ni ta dace! I'm the right one for her!" Taune haƙora Irfaan yyi yace, "She's not your type Anwar, you better forget about her or go bury your damn head in a grave!!" Dariya Anwar yyi yace, "But taji daɗin abunda nayi mata, ta tambaye ta da kanka. She tastes sweeter than any other woman..." bae ƙarasa ba yaji saukar naushi akan bakinsa gashi na da ɗinma bae warke ba gashi ya samo wani, taɓa bakin Anwar yyi yace, "Go On, ita zata fanshi duk abunda kk yi mun!" Shiru Irfaan yyi yana kallon Anwar dake murmushi despite bakinsa da yake zubar da jini profusely. Hanyar fita Anwar yabi yace, "Sae na mallaki Noor ko da amincewarka ko bbu!" Ficewa Anwar yyi ya bar Irfaan a tsaye, takaici ne yasa Irfaan jin zuciyarsa tayi baƙi ƙirin bae san lokacin da ya kaiwa bango naushi ba, bango bae fashe ba amma shi yaji ciwo amma ko zafi bae ji ba saboda ɓacin rai. Anwar ya shiga office ɗinsa ya shige cikin toilet ɗin dake haɗe da office ɗinsa, gaban mirror ya tsaya yana taɓa ciwon nasa, murmushi yyi kafin ya ciro first-aid box ya fara treating ciwon nasa, sosai yake jin sonta yana fusgarsa dan lokacin d ya hura mata iska a kunni wani noƙewa tayi kamar an taɓa gidan snail, hakan ya tabbatar masa da cewar Irfaan yyi ƙoƙari sosai wurin tarbiyyantar da ita kuma ƙila shys yake jin tsoron alaƙarsa da Noor ɗin, amma Anwar ya riƙa ya zama kamar ƙudan zuma ita kuma flower dan haka bbu abunda zae raba su, wani abunda ke sake burgeshi game da ita shine kunyarta da tsiwa. Murmushi yyi kafin ya fita ya duba patients ɗinsa yana tafe yana saƙa yanda zaeyi maganin Irfaan tunda baya jin lallama.

Irfaan kam ji yyi baze iya zaman asibiti yau ba hakan yasa ya ɗauki kayansa ya fice, kwana biyu ma bbu wasu severe cases so ƙananun Doctors ɗin suna iya handling komai, ɗazu dae yyi operation ɗin wani VIP da yafi son Irfaan yyi masa dan yafi yarda dashi, har ya kai bakin motarsa ya tuna ya manta da laptop ɗinsa, komawa yyi ya ɗauko laptop ɗin a hanyarsa ta dawowa ya tarar da Asmah, murmushi tayi masa sannan ta miƙa masa Invitation Card ɗinta, hannu yasa ya karɓa kafin yyi congratulating ɗinta ya juya yyi tafiyarsa, tsaye tyi tana kallonsa har ya ɓace kafin ta samu guri ta zauna, Allah Ma Yasan tana son Dr Irfaan amma Allah yyi ba ita bace matarsa hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya kafin ta miƙe tana sauke ajiyar zuciya. Very soon kafin auren zatayi submitting resignation later ɗinta, murmushi tayi wa kanta kafin ta juya tayi hanyar Nurse's Station.
Yana parking motarsa ya fito nan ya tarar da Asaad a parking lot ɗin yana neman gurin ɓoya, murmushi yyi ya ɗaukeshi sama yace, "Asaad! Where you Mum?" Dariya Asaad dake da kimanin shekaru ukku yace, "Un..cle Ir..faak, my mummy is in the living room.." murmushi Irfaan yyi yace, "Say Uncle Irfaaan with letter N at the end!" Muryar Zaynoora ya jiyo tana cewa, "Asaad! Yarona? Where are you?" Ta faɗa da sigar wasa, Asaad kuwa yana jin muryarta sae ya ƙara maƙelewa a ƙirjin Uncle ɗinsa, har ta ƙaraso gurin hannayenta ne a idanunta ta rufe su da alamar wasan ɓuya suke yi itada Asaad, tana jin warin asibiti kuwa tayi wa kanta fullstop tare da buɗe idanunta, tun ɗazu yake kallonta amma tana buɗe idanunta ya ɗauke kansa daga kanta, sauke Asaad yyi nan ya ruga da gudu ya rungume Zaynoora da ƙarfinsa, murmushi tayi masa ta sake rungumeshi. Ɗauke kai Irfaan yyi ya fara tafiya nan yaji Asaad na cewa, "Un..cle Irfaak picked me up!" Dariya ta fashe dashi jin yadda Asaad ya kira sunan Yaaya Irfaan, sarai Irfaan yaji lokacin da take dariya da sunan da Asaad ya kira shi amma haka ya ɗauke kai ya shige cikin gida. Yana shiga cikin parlourn ya tarar da Hajaarah da Aunty a zaune a parlour suna hira, yana shigowa ta durƙusa har ƙasa tace, "Yaya sannu da zuwa, Ina wuni!" Fuskarsa ɗauke da murmushi yace, "Lafiya Alhamdulillah, Ya mai gidan naki?" Murmushi tayi jin yanda Yaya ya koma kamar wani babban mutum daga yadda yyi tambayar, "Lafiyansa lau, yace na gaishe ka!" Kai ya ɗaga kafin ya kalli Aunty yace, "Sannu da gida Aunty!" Dariya tayi tace, "Lafiya lau likita bokan turai!!" Murmushi yyi kafin ya tura ƙofar part ɗinsa ya shige ciki.

Bae wani jima cikin ɗakin ba ya fice zuwa Masjid dan an fara kiran sallar Laasar, a gefen Ya Hajaarah Zaynoora ta zauna tace, "Yaya ni gaskiya bazan je islamiya ba yau ni, haka kawai na tafi na dawo kun tafi?" Taɓe baki Ya Hajaarah tayi tace, "Wallahi bbu ruwana sae Yaaya yazo ya sameki ko? Kiyi tafiyarki inya so idan anyi hutu ai sae ki zo kiyi mun hutu inace Asaad ne ai sae kin gaji dashi!" Turo baki Zaynoora tayi tana cewa, "Ni dai gaskiya bazan je ba!" Kallonta Aunty tayi tace, "Idan ko baki je ba sae na haɗa ki da yayanku!" Turo baki Zaynoora tayi cikin ƙunƙuni da ita kaɗai tasan me take faɗa tace, "Sae kace ina ruwanki, aikin banza kawai!" Tana faɗan haka ta gyara zamanta akan kujera daidai da shigowar Irfaan gidan kuwa, yana ganinta zaune a parlour yace, "Me kike yi baki tafi ba tun ɗazu?" Haɗe rai tayi ta miƙe tsaye zata wuce part ɗinsu, har tayi nisa yace, "Ke zo nan!" Juyowa tayi jin ta tokalowa kanta masifa, shi kansa wani haushinta yake ji ko kishi ne bae gama tabbatarwa ba yace, "Wa kike haɗewa rai?" Saurin sakin fuskarta tayi tace, "Ni ba haɗe fuska nake yi ba!" Ɗauke kansa yyi yace, "Ɓace mun da gani!" Ba shiri ta wuce ɗaki ta ciro hijab ɗin islamiyarta da jakanta, ba shiri ta fito tayi wa Ya Hajaarah da Asaad sallama kafin ta fice. Zama Irfaan yyi a parlourn riƙe da wayarsa a hannu ana hira amma sae ya ga dama yake saka baki, can ya ɗaga kansa daga wayar yace, "Ina Salma ne? Ban ganta ba yau gaba ɗaya!" Aunty dae ba ƙaramin farinciki da jin tambayar Irfaan, ɗan sakaya fuska tayi tace, "Salma ai bata jin daɗi amma ta ɗan samu bacci yanzu!" Kai ya ɗaga kafin yace, "Tasha magani kuma?" Saurin girgiza kai Aunty tayi tace, "Bata sha ba sae dae idan ta tashi baccin!" Shiru yyi bae sake cewa komai ba nan Hajaarah tace, "Allah sarki, Allah Ya bata lafiya!" Ameen duk suka rufa dashi kafin suka cigaba da hira abunsu.

Bayan malamin Hadisi ya fita daga ajinsu ne Zaynoora ta juya ta kalli Raudah tace, "Idan mutum yana kasa haɗa ido da mutum kuma yana jin zuciyarshi na bugawa da sauri idan yaga mutum me haka yake nufi?" Shiru Raudah tayi kafin tace, "Soyayyah mana, sae dae idan so ne a tsakaninsu!" Wani kalan tsaki Noor taja tace, "Dalla yi mun shiru kinsan me kike faɗa kuwa?" Harara Raudah ta watsa mata tace, "Toh da meye, baki san meye ba kuma ina faɗa miki kima yi mun rainin wayo!" Malamin Tauhidi ne ya shigo nan ajin ya ɗauki shewa dan matsahi ne sosai kuma yana da kyau, shiru ajin ya ɗauka saboda shigowar Wahidah, bbu wanda bae san malami Nura yana son Wahidah ba, tayi latti sosai amma haka Malam Nura ya kawar da kai wanda a ƙa'ida sae yyi mata bulala ukku, fara ce sosai ga gashin idanunta zaro zaro da manyan idanu sosai hakan yasa bbu iya shegen da bata iya ba da ido. Guri ta samu a kujerar dake bayansu Zaynoora da Raudah ta zauna, matsowa Raudah tayi daidai saitin kunnin Zaynoora tace, "Ga mae son Yayanki nan ta zo!" Wani ɗanyen takaici ne ya koro daga zuciyar Noor nan ta turɓune fuskarta sarai duk da Ummansu Wahidah ƙawar Mamansu Zaynoora ce, taɓota Wahidah tayi tace, "Ke! Ina ta yi miki magana bazaki kula ni ba?" Ɓata rai Noor tayi ta riƙo hannun Wahidahn kafin ta juya fuska a ɗaure tace, "Aw magana kika yi? Ai ban ji ki ba and karki ƙara cemun Ke ko baki san sunana bane?"

Hit the vote button lovelies!😘

©️Fateemah MG

????????????? ?????Where stories live. Discover now